Hukumar NSA Ta Bayyana Sunayen Ƙungiyoyin Da Suke Ɗaukar Nauyin Ta’addanci

Daga: Nura Ahmad Hassan

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo-Janar Babagana Monguno mai ritaya, ya bayyana sunayen wasu kungiyoyin da ke tallafawa kungiyoyin ta’addanci a yankin Sahel.

Monguno ya bayyana hakan ne a ranar Talata a jawabin da ya gabatar a taron karawa juna sani na kungiyar malamai da masu wa’azi da limaman kasashen yankin Sahel karo na 14 a Abuja.

“Ta’addanci da karuwar ayyukan ta’addanci daga kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi a yankin Sahel tun daga shekarar 2016, kungiyar ISGS ce ke jagoranta, wadda galibi ke aiki a Mali har zuwa Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso,” in ji shi.

“Ayyukan kungiyoyi irin su Jama’at Nasr al-Islam Wal Muslimin (JNIM), da Islamic and Muslim Support Group (GSIM), da ISGS, ke cigaba da yin barazana ga zaman lafiyar yankin.

“A Najeriya, Boko-Haram da Islamic State a yammacin Afirka (ISWAP) ne suka mamaye ayyukan ta’addanci, musamman a yankin Arewa maso Gabashin kasar.”

Halin da ake ciki a yankin Sahel, a cewar hukumar NSA, bai taba yin muni ba kamar yanzu, yayin da tashe-tashen hankula ke cigaba da yaduwa tare da karuwar yawan ‘yan gudun hijira da kuma karuwar karancin abinci.

A gare shi, akwai bukatar sake duba tare da sake tsara dabarun gwamnatocin kasashen waje da na shiyya-shiyya game da yankin Sahel da kuma ajiye munanan zato.

Monguno ya bukaci kasashen duniya da abokan huldar su na yankin Sahel da su ba da fifiko wajen gudanar da mulki, da yin taka-tsantsan wajen neman shimfida zaman lafiya ta hanyar tattaunawa, da kuma matsa kaimi ga daukar karin matakan da suka dace ta hanyar al’ummomin da abun ya shafa.

Sai dai ya bayyana cewa, an yi nazari kan yuwuwar ISWAP kafa daular halifanci ga kasashen da ke adawa da tafkin Chadi (LCBC) ta hanyar hadin gwiwa da karfafa kokarin kasashen yankin.

Ya kuma bayyana daukar bidiyoyin farfaganda da kungiyoyin ‘yan ta’adda suke yi don nuna kansu a matsayin masu fada a ji a yankin a matsayin wani yunkuri ne kawai na neman goyon baya daga masu goyon bayansu, yayin da suke fafutukar tabbatar da kansu.

“Saboda haka, an kiyasta cewa yayin da ƙungiyoyin ke riƙe da dogon lokaci dabarun manufar samar da halifanci, kokarin da kasashen LCBC za su cigaba da kawo cikas ga wannan burin,” Monguno ya ce.

“A dangane da haka, ya zama wajibi malamai, masu wa’azi, da shugabannin al’umma a yankuna su ba da muhimmanci ga kokarin jami’an tsaron mu, domin kawo karshen wannan barazana.

“Kamar yadda hadin gwiwa tsakanin gwamnatoci ke kara habaka cigaban jami’an tsaro wajen yaki da ta’addanci, ya kamata kawance da kokarin kungiya irinsu LOPIS su zama kashin bayan sake gina al’ummarmu da ta’addanci ya mamaye.”


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button