An Fara Biyan Kudin Makaranta Na KUST Wudil 2022

Daliban Makarantar KUST Wudil sun fara biyan kudin Makarantarsu na zangon Karatun shekarar 2022, biyan kudin makaranta wajibine kamar yadda kowa ya sani a duk shekara.

Dalibai da suke ciki ne suke biyan kudin makarantar a halin yanzu (returning students), tsarin biyan kudin makaranatar ya kasance za’a ayi shi ne ta shafin su na yanar gizo-gizo.

Related Articles

Ko wane Dalibi zai shiga cikin dashboard dinsa na Makaranta inda zaiga adadin abinda zai biya na kudin makarantar tasa a jimlance.

Biyan kudin makarantar akan lokaci abu ne mai matukar mahimmanci sannan akasin haka kuwa ka iya jawowa dalibi wata matasala, dan haka ana kira ga dukkan dalibai dasu hanzarta domin biyan akan lokaci.

Domin gujewa dukkan wata matsala wajen biyan kudin, sai a ziyarci cafés dake makarantar ko kuma café mafi kusa dakai a area naka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button