Education

Farashin Katin Jarrabawar NECO Ya Hauhawa 2022

Sponsored Links

Farashin katin Neco wato Token ko kuma ace PIN na bude jarrabawar neco ya hauhawa a cikin wannan sabuwar shekara da muka shiga ta 2022, wanda farshin ka iya karuwa sosai ga masu saye su sayar domin samun abin sanyawa abaka.

A yanzu farashin duk guda daya a shafin Neco ya koma izuwa N625, shekara da ta wuce ta 2021 farshin dai bai kai haka ba domin kuwa farshin na tsohuwar shekara shine 500 da wasu yan kwabbai.

Wannan Sanarwa ta fito ne daga shafin hukumar ta NECO inda ta rubuta Karin farashin kuru-kuru domin sanar da abokan hulda, iyaye da dalibai.

Jarrabawar dai ta Neco tana ta samun masoya duba da yadda kihiyar ta wato Waec tayi tashin gwauron zabo wannan ya janyo hankalin iyaye wajen zaben yi jarrabawar ta Neco.

A nan gaba kadan ake sa ran fitowar sakamakon jarrabawar na Private Neco inda za’a shiga sabon shirin zana sabuwar Jarrabawar ta 2022.

Muna fatan Farashin zai tsaya a iya Neco Token banda kudin zana jarrabawar ga wadanda zasu biya idan basu sami biyan gwamnati ba.

hausadrop

Aminu B Yusuf, Editor in Chief at HausaDrop.Com

Leave a Reply

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button