An Saki Sakamakon Jarrabawar WAEC Ta 2021

Hukumar shirya jarabawar kammala sakandare ta Afrika ta yamma, WAEC, ta saki sakamakon jarabawar da dalibai suka yi ta shekarar 2021.

TheCable ta ruwaito cewa, Patrick Areghan, shugaban hukumar jarabawar ta Najeriya, ya sanar da hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Ya ce jimillar dalibai 1,573,849 ne suka yi rijistar jarabawar a fadin Najeriya daga makarantu 19,425 da aka aminta da su. Yayin da dalibai 1,560,261 ne suka rubuta jarabawar.

Kamar yadda yace, 1,274,784 dalibai sun ci darussa biyar zuwa sama wadanda suka hada da Turanci da kuma lissafi.

Ya ce dalibai 1,560,261 sun ci darussa biyar zuwa sama a wasu darussan da ba Turanci ba da lissafi, TheCable ta ruwaito.

Areghan ya ce hukumar jarabawar ta rike sakamakon dalibai 170,146 da ta ke zargi da magudin jarabawa.

Ya kara da cewa, WAEC a halin yanzu ta gama tantancewa tare da sakin sakamakon dalibai 1,256,990, wanda shi ne kashi 80.56% na daliban da suka zauna jarabawar a Najeriya.

Areghan ya kara da cewa, a halin yanzu hukumar ta na tantance sakamakon dalibai 303,271 wanda ke wakiltar kashi 19.44% na dukkan sakamakon daliban Najeriya.

Hukumar jarabawar ta ce tsaikon da aka samu ya biyo bayan matsalar da wasu dalibai suka samu da darussansu.

Areghan ya kara da cewa, dalibai na bukatar wasu lambobi daga hukumar tare da lambar jarabawarsu domin duba sakamakon ta yanar gizo.

An yi jarabwar wannan shekarar ne tsakanin watan Augusta zuwa na Oktoba, duk da na kammala jarabawar a karshen watan Satumba a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button