JAMB Ta Saki Sakamakon Jarrabawar Bana Na 2022

Hukumar JAMB mai shirya jarrabawar neman shiga manyan makarantun gaba da sakandire a Najeriya, ta sanar da sakin sakamakon jarrabawar da dalibai suka zana a bana.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Dr Fabian Benjamin ya fitar  ranar Asabar a Abuja, babban birnin tarayya.

A cewarsa, wadanda suka rubuta jarabawar za su iya duba sakamakon da suka samu ta hanyar tura sakon UTMERESULT zuwa ga lambar 55019 daga wayoyinsu salula.

Sai dai ya bayyana cewa har yanzu ba a saka sakamakon ba a yanar gizo saboda wasu ‘yan dalilai, inda suka bukaci dalibai da su duba sakamakon ta hanyar amfani da wayoyinsu na salula.

“Da zarar an tura sako ta amfani da wayar salula nan take mutum zai ga sakamakon da ya ci a jarabawar da ya rubuta ta shekarar 2022, kuma wannan ita kadai ce hanyar da mutum zai iya duba jarabawarsa saboda har yanzu ba a saka sakamakon ba a yanar gizo saboda wasu dalilai.

“Ina kuma gargadin wadanda suka rubuta jarabawar da su yi hattara da ‘yan damfara da ka iya turo musu sako na cewa za su iya duba musu sakamakon su ta wasu hanyoyi.

“Har ila yau hukumar ta yi kira ga wadanda suka zana jarabawar da su yi hattara da irin wadannan sakonnin da za su iya samu domin gudun saka su cikin rudani” in ji shi.

Benjamin ya kara da cewa hukumar ta yi hakan ne domin saukaka duba sakamakon jarabawar ga wadanda suka rubuta.

Ya kara da cewa an samar da wannan hanyar mai sauki ce domin hana wasu masu shagon kasuwancin intanet da ke muzgunawa masu duba sakamakon jarabawar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN dai ya ruwaito cewa an gudanar da jarabawar ne daga daga ranar Juma’a 6 ga watan Mayu zuwa 13 ga Mayun na 2022.

One Comment

  1. Maii Dan Allah me dalilin kin sake sakamakon jamb gaskiya baayi mawasu adalciba domin dayawa sunyi amfanida lambobin sune nashekarar datawuce kuma wasu lamban tabace wasukuma anrufemusu layi
    Yakamata a dora sakamako online

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button