Education

Hukumar Jamb Ta Sanya Ranar da Za’ayi Printing Na Examination Slip 2022

Sponsored Links

Bayan kammala rjistar Jamb 2022 ta bana dukkan dalibai sun koma gefe suna ta tilawar abinda zasu iya cin karo dashi a yayin gudanar da jarrabawar ta bana duk da hukumar bata bude wajen printing Slip din ba wanda shine abu na karshe dalibi zai fitar domin sanin inda zai zauna tasa jarrabawar.

Saidai a yau ne hukumar ta JAMB ta fitar da wata sanarwa a shafinta na sada zumunta na twitter inda take cewa “Ana dab da fara printing na UTME slip 2022”

Wannan bayanai ya nuna cewa abun yazo inji  mai tsoron wanka! Dan haka dukkan dalibai sai su kara zage dantse kuma su kara kaimi domin tunkarar jarabbawar ta bana domin kuwa hukumar bata fadi ranar ba amma ta nuna cewa abun yana kusa sosai.

Sannan a wani bangaren daban kuma an gargadi dalibai mata das u guji amfani da kunshi mai a lokacin jarrabawar domin kuwa yatsu basu cika daukar na’urar thumb print ba kuma duk wace batayishi ba ba zata zauna jarrabawar ba.

Source: ArewaTalent

hausadrop

Aminu B Yusuf, Editor in Chief at HausaDrop.Com

Leave a Reply

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button