Ya Bukaci ’Yan Sanda Su Daure Shi Don Kubuta Daga Matarsa A Gida

Wani magidanci da ke zaman takura a gida a Italiya ya gabatar da kansa a barikin ’yan sanda, inda ya bukaci a sakaya shi a cikin sel (dakin ajiye masu laifi) saboda takurar da yake fuskanta daga matarsa a gida wadda ya kasa jurewa, kamar yadda daya daga cikin jami’an ’yan sanda ya bayyana wa manema labarai.

Magidancin dan asalin kasar Albaniya mai shekara 30 da ke zaune a garin Guidonia Montecelio, a birnin Rome a kasar Italiya, “Ba ya iya jurewa kan tilasta kansa zama tare da matarsa,” kamar yadda wata sanarwa da wani dan sandan Carabinieri daga birnin Tivoli da ke makwabtaka da mutumin ya bayar.

’Yan sandan yankin sun fitar da bayanin cewa, “Abin da ya fusata magidanci game da lamarinshi ne, ya gwammace ya tsere wa matar daga gidan, hakan ya sa ya gabatar da kansa ga jami’an Carabinieri don neman a sakaya shi a dakin masu jiran hukunci bayan aikata laifi.”

Jami’an ’yan sandan sun rubuta cewa, “Mutumin ya kasance a tsare a gidan ne, saboda samun shi da laifukan ta’ammali da miyagun kwayoyi na wasu watanni kuma yana da shekaru kadan a gurfanar da shi,” a wani jawabi da Kyaftin Francesco Giacomo Ferrante na birnin Tivoli Carabinieri ya shaida wa Kafar Labarai ta AFP.

“Yana zaune a gida tare da matarsa da iyalansa. Hakan dai bai yi kyau ba,” inji Ferrante.

Magidancin ya ce, “Saurara, rayuwar gida ta zamar min tamkar jahannama, ba zan iya kuma zama a gidan ba, ni so nake yi a kai ni gidan yari.”

Nan take aka kama mutumin saboda saba dokar zamansa a gidansa da ya aikata, hukumomin shari’a sun ba da umarnin a kai shi gidan yari.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button