Ranar Lahadi Za A Fara Fafata Gasar Kofin Afirka

A ranar Lahadi ne za a fara fafata Gasar Kofin Afirka na bana, mai suna AFCON 2021, kasancewar a bara ya kamata a buga, amma annobar coronavirus ta hana.
Wannan shi ne karo na 33 da za a buga gasar, sannan kasar Kamaru ce mai masaukin baki, sannan Total Energy Africe ne zai dauki nauyin gasar.
Kasar Aljeriya ce ke rike da Kofin, sannan kasar Misra ce ta fi kowace kasa lashe gasar, inda ta lashe sau bakwai.
A wasan farko, Kamaru ce za fa bude da kasar Burkina Faso a filin wasa na Olembe.
Binciken Bakin Raga ya gano cewa ba a doke kasar Burkina Faso ba ko sau daga a wasan neman gurbin shiga gasar.
Sai dai a haduwar kasashen biyu na karshe, Kamaru ce take samun nasara.
Najeriya a gasar: Wasan Najeriya na farko
A ranar Talata mai zuwa ce Najeriya za ta fara wasanta na farko, inda za ta fafata da kasar Misra.
Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta samu tsaiko a shirye-shiryenta na tafiya gasar, inda aka canja koci, sannan ta rasa manyan ‘yan wasanta da ake sa ran sa su taimaka mata sosai.
An kara kudin gasar
A wani cigaba da aka samu, Hukumar Kwallon Afirka, CAF ta kara kudin da ake ba zakarun gasar.
A ranar Juma’a da ta gabata ce Kwamitin Zartarwa na Hukumar CAF din ta zauna, inda ta amince da karin.
Shugaban Kwamitin, Patrice Motsepe ne ya sanar da karin, inda ya ce kasar da ta lashe za ta samu kudi $5 million, Karin $500,000 ke nan akan kudin da aka ba Aljeriya da ta lashe gasar a wancan karon.
Na biyu za ta samu $2.75 million, kasashen da suka kai wasan kusa da karshe za su samu $2.2 million, sannan wadanda suka kai wasannin kusa da wasannin kusa da karshe za su samu $1.175 million kowannensu.
Filayen da za a buga wasannin
Za a buga wasannin a filaye guda shida.
Filayen su ne na Olembe da za a bude gasar a birnin Yaounde, sai Stade Ahmadou Ajidjo da ke Yaounde, sai Japoma da ke Doula, da Limbe da ke Limbe da Kouekong da ke Bafoussam da Roumde Adjia da ke Garoua.
Za a yi amfani da na’urar VAR a gasar
A karon farko, za a yi amfani da na’urar taimakon rafare na VAR a Gasar Kofin Afirka a dukkanin wasannin gasar guda 52 maimakon na shekarar 2019 da aka fara amfani da na’urar daga wasannin kusa da na kusa da karshe.
For the first time in the history of the Africa Cup of Nations, Video Assistant Referees (VAR) will be used at all 52 matches, in Cameroon