Alfanu Da Matsalolin Tiktok Ga Rayuwar Matasa

Barkanku da kasance wa tare da shafin Taskira, shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban daga kowanne bangare, kama daga fannin zamantakewar aure, rayuwar matasa (Soyayya), rayuwar yau da kullum, da dai sauransu.

Tsokacin yau zai yi duba ne game da Shafin ‘Tiktok’, Shafin da dinbun matasa ke ya yi a yanzu, shafin da ya zama tamkar dandalilin siye da siyar wa musamman ga mata, ta yadda wasu ke baje kolin hajar tsiraicinsu.

Shafin da a kullum yake samun sabbin baki ‘yan yayi masu maida baya ta dawo gaba (Kara’i) wato matan aure. Shafin Tiktok shafi ne da a yanzu mata ke cin karansu babu babbaka, ba ga manyan ba, ba ga kananan ba. Da yawan mata sun tattara ga shafin Tiktok wajen neman mabiya (Fans) ta kowacce hanya, wanda ya zame musu abin ya yi na musamman.

Sai dai hakan ba ya tsaya ne iya ‘yan mata kawai ba, har ma da matan aure, su kan fito su nuna nasu salon da sunan wayewa. Shafin Tiktok shafi ne da ya hadar da mutane daban-daban na kowanne nahiya kamar dai yadda sauran shafukan sada zumunta ya kasance, sai dai ‘Tiktok’ ya zo da nasa sabon salon da ya bambanta da sauran shafuka, wanda malamai da sauran manya ke kokawa da tsarinsa wajen bata tarbiyyar al’umma.

Duk da hakan wasu na ganin cewa hakan ba wai bata tarbiyya bane, abu ne na ya yi kamar yadda komai ke sauyawa na rayuwa.

Tiktok abu ne na nishadi kamar yadda aka san sauran kafafen sada zumunta, sai dai kuma tsarin da mafi yawan masu yinsa suka daukar wa kansu sam! bai dace ba domin hakan ba tarbiyya ba ce, ba wayewa ba ce, ba hanya me bullewa ba ce, sai ma zubda mutunci.

Da yawan mabiya shafin sun gurbata tarbiyyarsu ta yadda suke zubda mutubcinsu da kuma addininsu sun koma tamkar wasu dabbobi ko marasa iyaye wanda suka rasa mafada, duk da cewa ba duka aka taru aka zama daya ba, akwai na kwarai masu yin abubuwan nishadi da nasihohi, da yabo da sauransu.

sai dai mafi yawan rinjayen matan musulman da ke bata tarbiyya sun nunka yawan masu kamalar ciki. Duk da irin kokawar da malamai ke yi akan shafin Tiktok, abin kara ta’azara yake a kullum, ta yadda ake kara fito da sabbin tsare-tsare da salo kala-kala dan kara bunkasa shi.

Wannan yasa shafin Taskira ya ji ta bakin wasu daga cikin matasa game da yadda suka dauki ‘Tiktok’ a wajensu, ko ya suke kallon matan da suke zubda mutuncinsu a ‘Tiktok’ ?, Ko za su iya auran ‘Yan Tiktok?, shin ‘yan ‘Tiktok’ na birge su?, ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:

Sunana Fadeelah Yakub (Milhat):
A ganina Tiktok bala’i ne, annoba ne, wanda ya zo mana sai dai mu ce Innalillahi wa Inna ilaihirraji’un, Allah ya yi mana tsari da shi, wadanda kuma suke yi Allah ya ganar da su ya shirye su, ko kadan ba sa birge ni.

Akwai wadanda suke amafani da shi wurin isar da sakonni masu kyau wanda za su amfani jama’a wadan nan sam! ba ni da matsala da su, amma a cikin kaso dari kashi casa’in da tara da digo tara suna amfani da shi ne wurin sabawa Allah, suna zub da mutuncin su musamman matan hausawa bai tsaya a iya ‘yan Mata ba har da matan aure sa zawara, so ni banga abun birgewa a gun sabawa Allah ba.

A’a ba zan iya auren dan tiktok ba dalili kuwa shi ne ina so na samawa ‘ya’yana uba na gari wanda za su yi alfahari da shi a duk in da suka tsinci kansu ba su rika jin kunyar nuna shi ba, wanda yake rawa a ‘Tiktok’ kamar dan daudu ta ina zai zama uba na gari? Allah ka bamu mazaje na gari wanda za mu yi alfahari da su duniya da lahira, ameen. Shawara ta gare ku ‘yan ‘TikTok’ musamman ‘yan uwana Mata, ku ji tsoron Allah ku sani rayuwar mace gajera ce, ki sani duk abin da kike yi yana nan a ajjiye ko da shekaru dari za su yi wataran ‘ya’yan ki za su gani shin me za ki ce musu idan suka ga fitsarar da kika yi da sunan wayewa? Allah ubangiji ya shirye mu gaba ki daya sannan ya kare mu da kariyar sa, Ameen.

Sunana Queen Nasmah daga Jihar Zamfara:


A zahiri ‘Tiktok’ a wannan lokacin wata jarabta ce ko in ce kaddara, in takaita ma zan iya kiran haka da masifa ce wadda ta tunkaro rayuwarmu ko in ce karnin da muke na karshen zamani. ‘Yan ‘Tiktok’ ba su taba birge ni ba, a takaice ni ko ‘Tiktok’ ban taba ajjiye wa a wayata ba, ballantana ayi maganar in yi ‘Tiktok’.

Babu abin da zai hana ni auren dan ‘Tiktok’ idan kaddarata auren shi ce, dan addini bai ce a guje mutum idan yayi kuskure ba, jawo su ake yi a jiki har su gyara, bayan haka ba duk dan ‘Tiktok’ bane gurbatacce wasu ke bata wasu. Shwarawata ga ‘yan ‘Tiktok’ masu zubar da mutuncinsu shi ne su ji tsoron Allah, shi ne ya halicce ki har ya yi miki arzikin lafiyar da kike abin da kika ga dama lokacin da wasu ke asibiti suna halin rayuwa ko mutuwa, dama ce Allah ya baku kar ku yi amfani da ita yadda bai dace ba.

Sunana Nabeela Dikko:


Maganar gaskiya a halin yanzu ‘Tiktok’ ya zama ruwan dare-game duniya kuma wata gagarumar hanyar yada badala, sai dai mu yi ta addu’a Allah ya kawo mana karshen wannan jarabawar ya kare mu da iyalan mu, ma su yi ya ganar da su gaskiya su daina. ‘Tiktok’ bai taba birgeni ba, hakan ‘yan tiktok din basa birgeni, don na dauke su marasa hankali wanda su ka dauki hanyar yahudu da nasara, su na bata lokacin su a banza. Ko alama ba zan yi gangancin hakan ba. Shawarata ita ce su ji tsoron Allah su daina su sani ko da rai ko ba rai duk abubuwan da suka aikata suna nan, wataran ‘ya’ya da jikoki za su kunna su gani, tom maganin kar ayi kar a fara idan kunne ya ji jiki ya tsira.

Sunana Sanaz Deeya daga Kazaure:


A ko wace manhaja akwai bata gari sai dai na ‘Tiktok’ ya fi daukar hankalin mutane, kasantuwar ita manhaja ce da ake saka bidiyo kadai. Ba kowa ne ke birge ni a ‘Tiktok’ ba, duk wanda ke abubuwa na banza to baya birgeni, ina yin ‘Tiktok’, kuma na dauki ‘Tiktok’ a matsayin dandalin nishadi, bana kallon ‘Tiktok’ a matsayin wata gurbatacciyar manhaja, sai dai in ce akwai gurbatattu masu zubar da mutunci a ciki, amma ba duka aka taru aka zama daya ba. Zan iya auren dan ‘Tiktok’ matukar yana da halaye na gari. Shawarar da zan bawa matan ‘Tiktok’ masu zubar da mutunci shi ne su ji tsoron Allah, kuma su sani duk abin da suke yi wata rana ‘ya’yansu za su gani, kuma dole abin da ka shuka shi za ka girba. Sannan kuma bayan rayuwa akwai mutuwa, akwai rayuwar barzahu sannan akwai lahira, yana da kyau duk abin da za ka aikata ya zamana cewa kana tuna lahirarka, fatan za su ji tsoron Allah su kuma daina zubar da mutuncinsu, domin ita ‘ya mace tana da kima da daraja.

Sunana Musa Yakub Malam (Mr My):


kowani abu yana da ‘adbantages’ da ‘disadbantages’, ana duba wanda ya fi rinjaye ne sai a yi masa hukunci. To a gaskiya ‘disadbantages’ din ‘Tiktalk’ ya fi ‘adbantage’ din sa yawa. Duba ga irin dama da mata suka samu na nuna tsiraicinsu, cudanya da mazan banza da saura su wanda hakan ya sabawa addinin musulunci. Wasu daga ciki suna birge ni, musamman wanda suka dauki kafar wajen wa’azantar wa da kuma ilmantarwa. Sosai ma kuwa zan iya auren ‘yar ‘Tiktok’ da tsarkakakkiyar niyya In dai hankalina ya kwanta da yadda take. Mace tsarkakakkiyar halitta ce mai daraja, babu addinin da ya yadda da nuna tsiraici. Ina mai ba wa duk masu irin wannan dabi’ar shawara da su daina. Allah ya shiryemu baki daya.

Sunana Musbahu Muhammad Goron Dutse Jihar Kano:


Yin ‘Tiktok’ ba laifi bane nishadi ne amma raye-rayen banza da fadace-fadace tsakanin mata. Kuskure ne babba kuma illa ne ga rayuwar su. Ni ina yin ‘Tiktok’ amma maganar gaskiya matan ‘Tiktok’ ba sa birge ni ko kadan wallahi. Idan har bata rayuwar iskanci, bata yada kalmomin batsa, bata fadace-fadace toh zan iya. Shawata su ji tsoron Allah su kiyayi rudin shaidan sabida akwai ranar da za mu koma ga Allah, kuma za a yi wa kowa hisabi akan abin da ya aikata.

Sunana Abbas daga Jihar Gombe:


Eh! gaskiya ni a ganina yin ‘Tiktok’ a wannan zamanin bai dace ba saboda yadda suke sa kayan da bai dace ba kuma suna rawa suna turawa, wannan ya sabawa addini da al’ada. Eh! wasu daga ciki suna birge ni, wasu kuma ba sa birge ni, ‘Tiktok yana ba da nishadi matuka. A’a gaskiya ba zan iya aure ‘yar tiktok ba saboda suna tikar rawa suna tura wa idan muka haifi ‘ya’ya wata rana za su iya ganin hoton uwarsu tana rawa. To shawara anan shi ne su tuba su koma ga Allah saboda shi Allah mai karbar tuban bayinsa ne.

Sunana Abdullahi Dahiru Matazu Daga Jihar Katsaina:


Yadda na dauki matan tiktok a da, na dauke su a matsayin nishadi. Amma yanzu idan na hau ‘Tiktok’ na ga yadda ‘yan mata ke cincirindo sai na ce Allah ya sauwake na dauke su tamkar masu tallan kansu ta kowacce fuska. ‘Yan ‘tiktok’ basa birge ni. Saboda mafi yawancin su za ku ga suna daukar bidiyo babu hijabi wanda wannan haramun ne a musulunci. Da ina yi amma yanzu kam ko sha’awa bana yi. Zan iya auren ‘Yar tiktok saboda na san cewa taimakon ta zan yi kuma idan na yi hakan kamar na yi jahadi ne. Shawara ta zuwa ga Matan ‘Tiktok’ ku kara zage damtse akan cewa za ku iya barin ‘Tiktok’ a ko da yaushe, ku ji tsoron Allah kuna karya dokar sa. Allah ya kara kiyaye mu amin ku kasance da Taskira a ko da yaushe

Sunana Mansur Usman Sufi, Sarkin Marubutan Yaki daga Jihar Kano Nijeriya.:
Yin tiktok ga mata abu mai kyau
Abun dubawa kawai shi ne mene ne abin da suke aikata wa? sai dai mafi yawan wasu matan sun mayar da ‘tiktok’ din wajen tallata tsiraicin su Allah ya kiyaye ya shirye mu baki daya Amin. Tiktok bai taba birge ni ba bisa dalilin hakan ya sanya bana yin shi, saboda haka ma ban dauke shi da muhimmanci ba, domin harka ce ta wasa mafi yawa a tiktok. Zan iya auren ‘yar ‘Tiktok’ sosai kuwa, mene ne dabi’unta a ‘Tiktok’ shi ne abin dubawa, za ka samu wasu matan da basa ‘Tiktok’ ba nagari ba ne amma za ka samu mai yin ‘Tiktok’ mutuniyar kirki, ba ‘Tiktok’ ne matsala ba mene abin da take aikatawa a ‘Tiktok’ kuma mene ne dabi’un ta, A ko ina mace ta gari nake so Allah ya bani ko da ‘yar ‘tiktok’ ce. Shawara da zan bawa mata masu zubar da mutuncinsu a ‘Tiktok’ shi ne su sani cewa duk abin da suka aikata Allah zai tambaye su a gobe kiyama, kuma sun yi watsi da daraja da Allah (SWT) ya yi masu a matsayin su na iyaye mata da su ne za su koyar da tarbiyya, Wani abu mafi muni da ban tsoro da ya kamata su fahimta shi ne duk bidiyon da kika saki na tsiraici ba ki sani ba zuwa ina ne zai yadu a duniya?, Ko da kuwa kin goge bidiyon watakila kina kwance a kabari kuma mummunan aikin ki yana yawo a duniya subhanallah don Allah su ji tsoron Allah su tuna cewa su ne iyayen al’umma masu yi mana tarbiyya

Allah ya bamu dacewa Amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button