Wata mata mai suna Zainab Bello ta kammala karatun digiri na Mathematics da first class bayan tayi aure ta haihu

Wata matar Aure mai suna Zainab Bello Kofa ta kammala karatun digiri a jami’ar Ahmadu Bello University Zaria bayan tayi aure kuma ta haihu.
Inda ta karanta Lissafi (Mathematics) ta fito da sakamako mafi daraja a ABU Zaria inda ta samu maki 4.85 -CGPA.
Zainab Bello dai matar aure ce kuma tana da yara sai da tayi aure kafin ta fara karatun jami’a, amma cikin ikon Allah gashi ta zama the best a ajin Mathematics.
A wani bangaren kuma labaran da wasu majiyoyin suka fitar sun bayyana cewa, Zainab Bello Kofa, ita hafiza ce domin ta harda ce Alkur’ani mai girma tun tana yar shekara sha daya 11 a duniya.
Wanda idan tabbas gaskiya ne to ba abin mamaki bane zata iya samun makin karatunta na lissafi fiye da haka duba da daraja da mu’ujizar Alkur’ani mai girma.
Source: DalaTopNews