Kwanan Nan Za Mu Kara Wa Malaman Makaranta Albashi – Gwamnati
Gwamnatin Tarayya ta ce nan ba da jimawa ba za ta fara aiwatar da shirin karin albashin da za ta yi wa malaman makaranta.
Minista a Ma’aikatar Ilimi, Chukwuemeka Uwajiuba, ne ya bayyana hakan ranar Alhamis, yayin wata tattaunawa da ba da shaida ga malaman makaranta da kamfanin Seplat ya horar a birnin Benin na Jihar Edo.
“Tsarin albashi na musamman ga malaman makarantun firamare da na sakandire, ciki har da shiri na musamman ga malaman da aka tura yankunan karkara, malaman kimiyya da sauran wasu tsare-tsare na musamman ga malaman, nan nan tafe nan ba da jimawa ba,” inji shi.
Ministan, wanda mai taimaka masa ta musamman Misis Muna Onuzo-Adetona, ta wakilta, ya ce gwamnati mai ci na yin iya bakin kokarinta wajen tallafa wa bangaren ilimi, musamman wajen magance kalubalen da malamai ke fuskanta.
A cewar Ministan, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fito da nagartattun manufofi da suke dab da kawo sauyi a bangaren ilimi, musamman ma a bangaren inganta walwalar malamai, ta yadda za su yi gogayya da takwarorinsu a kasashen duniya.