Kotu Ta Ce Ba Wanda Ya Tursasa Abdulmalik Tanko Ya Ce Shi Ya Kashe Hanifa

Kotu ta yi watsi da ikirarin Abdulmalik Tanko ya yi cewa ba a cikin hayyacinsa ya fada mata cewa shi ne ya kashe dalibarsa mai shekara biyar, Hanifa Abubakar ba.

A yanzu haka kotun na shirin yanke hukunci kan Abdulmalik Tanko kan zargin kashe dalibar tasa wadda ya yi garkuwa da ita.

Alkalin kotun da ke sauraron shari’ar kisan Hanifa zai yanke wa Abdulmalik Tanko hukunci ne bayan tabbatar da cewa babu wanda ya tursasa wanda ake zargin fadar cewa shi ya kashe ta a karon farko.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button