Na rantse babu wanda zai saci ko kwabo idan na zama shugaban kasa, Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takaran kujeran shugaban kasa karkashin Peoples’ Democratic Party PDP, Atiku Abubakar, ya rantse da Allah cewa zai tabbatar da cewa babu wanda yayi sata idan ya zama shugaban kasa a 2023.

Hakazalika ya yi alkawarin cewa zai mayar da hankali kan lamarin ilmi kuma ya kawo karshen yajin aikin da Lakcarori ke yi.

Atiku ya bayyana hakan ne yayinda ya kai ziyara jihar Rivers don tattaunawa da Deleget din jihar a birnin Fatakwal, rahoton Punch.

Atiku ya bayyana bacin ransa kan yadda dubunnan dalibai ke zaune a gida saboda gwamnatin APC ta sace kudin da ya kamata ace anyi amfani da su wajen gyara sashen Ilmi.

Yace:

“Zan tabbatar da cewa an sa ido sashen Ilimi. A yau an kulle dukkan jami’o’i tsawon watanni yanzu. Saboda suna sace kudin. Zan tabbatar da cewa babu wanda zai sace kudi, na ranste.”

Tsohon mataimakin shugaban kasa yace gwamnatin APC ta raba kawunan yan Najeriya kuma ta tsananta matsalar tsaro.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button