Kada ku ga laifin wadanda su ka kashe Deborah, ta ƙetara iyakar da ba’a ƙetarawa a musulunci – Inji Farfesa Ibrahim Maqari
Farfesa Ibrahim Maqari, limamin babban masallacin Abuja, yayi hukunci akan mummunan kisan da aka yi wa ɗalibar nan Deborah Samuel, wacce ake zargin da yin ɓatanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW), da kuma keta haddin musulunci.
Ibrahim Maqari ya nuna ɓacin ran sa kan abinda ɗalibar ta yi
Jaridar Gazetteng ta rahoto cewa, da yake wanke masu laifin, Ibrahim Maqari ya yi karin haske akan fushin hukuncin da zai hau kan duk wanda ya keta haddin addinin musulunci, domin a cewar sa baza’a ci gaba da jurar irin wannan halayyar ba.
Dole ne kowa ya kwana da sanin cewa mu musulmai muna da wadansu iyakoki masu hadari da ba’a ketara su, mutuncin shugaban mu Annabi Muhammadu SAW, yana gaba-gaba a cikin irin wadannan iyakokin. Idan ba’a share mana fushin mu ba, to baza’a kalubalance mu ba domin mun share wa kanmu da kanmu, ” ya fadi hakan ne a shafin sa na tuwita.
Anja kunnen masu son taɓa mutuncin musulunci
Haka kuma wani jami’in gwamnatin jihar Sokoto, mai suna Anas Mohammad Sani, ya yi jan kunne ga mabiya addinin kirista, cewa su kiyayi yin maganganu na rashin ɗa’a ga fiyayyen halitta manzon Allah (SAW)
Musulmai basa daukar rainin batanci ga Annabi Muhammad SAW. ” Yayi gargadi