Matashi Ya Yi Yunkurin Kashe Kansa Saboda Budurwarsa Za Ta Auri Wani

Wani matashi a Kano ya yi yunkurin kashe kansa ta hanyar shan guba saboda mai kudi ya kasa shi a wurin budurwarsa.

Matashin mai shekara 26 wanda dan unugwar Gama da ke Karamar Hukumar Nasarawa, ya kwankwadi fiya-fiya ne bayan budurwar tasa ta yi watsi da shi ta koma wa wani wanda ya fi shi kudi da ta ce ya fi shi iya soyayya.

Related Articles

Wani ganau ya ce matashin, wanda ke harkar sayar da waya a kasuwar Farm Centre, ya tsallake rijiya da baya ne bayan wansa ya riske shi yana cikin shan fiya-fiyar.

Ya ce, wan nasa, “Yana ganin shi yana sha sai ya zo da sauri, mutanen da ke wurin suka taimaka aka kwace kwalbar fiya-fiyar daga hannunsa.”

Da yake magana bayan an ceto rayuwarsa, Tijjani ya ce ya ce yanke shawarar kansa ne saboda ba zai iya rayuwa ba tare da budurwar tasa da ta juya masa baya ba.

Ya ce, “An fada min cewa za ta auri wani ba ni ba, kuma yar ya tura iyayensa domin tattaunawa da iyayenta a kan hakan. Shi ne kawai na yanke shawara, domin ba zan iya ganin ranar aurenta ba.”

Zuwa lokacin da muka hada wannan rahoto dai ba mu samu wani karin bayani daga ’yan sanda ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button