Ayaba, kankana da jerin abincin da suke taimakawa maza wajen kwanciyar aure.
Ga ma’auratan da suke bukatar inganta rayuwar kwanciyar aurensu, akwai wasu jerin abinci da masana sukayi bincike suka ce ya kamata mutum ya rika mu’amala da su sosaii domin ingancin lafiyarsa.
A binciken da masanan sukai sun ce daga cikin abubuwan da suke jawo karfin namiji a gidan aure ya yi qasa akwaisu suke kamar:
- Gajiya.
- Rashin sukuni.
- Shiga halin lahaula.
- Da kuma shan kwayoyi.
Wani shahararren likita ya kawo wasu kayan abinci da za su taimaka wa duk wani magidanci.
1. ‘YA ‘YAN KABEWA.
‘Ya ‘yan kabewa za su taimaka wa namiji da sinadarin zinc wanda yake inganta ruwan sinadarin ‘da namiji, kuma yana kara mai a jikin mutum.
Za a iya jefa ‘ya ‘yan kabewa a abin sha a lokacin kalace, ko kuma a cikin kayan ganye kamar su salak da sauransu.
2. NAMA.
Irinsu naman saniya yana dauke da wani samfuri na nau’in Amino acid da ake kira da (L-Carnitine), wanda yana taimaka wa wajen kara karfin gaba.
3. AYABA.
Ayaba tana dauke da sinadarin Vitamin B wanda yana rage gajiya a jikin ‘Dan Adam. Haka zalika ayaba na dauke da Tryptophan da Potassium da ke kara lafiya.
A jikin ayaba akwai sinadarin Bromelain wanda aka ce yana kara karfin gudanar jini a jikin mutum.
4. COCO.
Masana ilmin lafiya sun ce cin Coco ko kuma cakulet da aka sarrafata da sinadarin na Coco yana aiki a matsayin kayan maza saboda sinadaran Phenols da Phenylethylamine.
5. KWALLAYEN GYADA.
Yawan cin kwallayen gyadan kashu da almond za su iya taimakawa magidanci wajen qara qarfin maza. Masana sun ce wadannan abubuwa suna da mai da kuma sinadarin L-Arginine.
6. KANKANA.
A wani bayani da wani babban likita yayi wanda yayi karatu a School of Nursing under the Department of Chemistry Integrated Science me suna Doctor Chodry zango ya fitar, ya nuna ceqa kankana tana cikin kayan marmarin da suke kara qarfin lafiyar namiji domin ruwansa na dauke da L-citrulline.
7. Kwai.
Masana sun ce kwai yana magance matsalolin ‘da namiji a gidan aure domin yana dauke da wani samfurin Amino Acid da masanan su ke kira da L-arginine.
MUNGODE DA KASANCEWA DA HAUSADROP.