A Shirye Muke Mu Mika Abba Kyari Ga Amurka Idan Bukatar Haka Ta Taso — Malami

Ministan Shari’a na Kasa, Abubakar Malami, ya ce hukumomin tsaron Najeriya a shirye suke su mika dakataccen jami’in dan sanda Abba Kyari ga hukumar tsaron Amurka ta FBI, da zarar sun bukaci hakan.

Malami ya bayyana haka ne a wata tattaunawarsa ta musamman da gidan talabijin na Channels, a ranar Talata.

A cewar Ministan, “Akwai abubuwa masu yawa da mu ke dubawa, ciki har da yiwuwar mika Abba Kyari ga Amurka, matukar bukatar hakan ta taso.

“Wannan batu ne da ya shafi yin aiki tare tsakanin kasa da kasa kuma muna aiki tare da su a kan haka, sannan ana samun ci gaba,” cewar Malami.

Ministan ya kuma tabbatar da cewar hukumomin Najeriya na aiki tare da jamian Amurka kan tuhume-tuhumen da ake wa Abba Kyari kan alakarsa da dan damdarar nan na Intanet, Abbas Raymond, wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Sai dai Malami bai ce komai ba kan abin da gwamnatin Najeriya za ta yi idan Amurka ta bukaci a mika mata Abba Kyari in ban da cewa kawo yanzu kasashen biyu na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin

Binciken da aka fara gudanarwa kan alakar Kyari da Hushpuppi ya yi sanadiyyar dakatar da Abban daga aikin dan sanda dungurungum.

Shi kuwa Hushpuppi hukumar FBI ta tsare a wani gidan yari da ke can a kasar ta Amurka.

Source: Aminiya Dailytrust

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button