Kotu Ta Daure Matashi Saboda Satar Tukunyar Jar Miya Da Nama Zuku-Zuku A Ibadan

Ibadan – Wata kotun Majistare da ke zamanta a Ibadan, a ranar Laraba ta yanke wa wani mutum dan shekara 23, Isaac Dumabara, hukuncin daurin wata daya saboda satar tukunyar jar miya da nama da kudinta ya kai N40,000 daga wurin sayar da abinci.

Alkalin kotun S.A. Adesina, wanda ya samu wanda ake zargin da laifin sata, ya yanke masa hukuncin zaman gidan yari na wata daya ba tare da zabin biyan tara ba, Premium Times ta rahoto.

Tunda farko, dan sanda mai shigar da kara, Sikiru Ibrahim, ya shaida wa kotun cewa Mr Damubara kuma ya sace tukunyar gas, stablizer da takalma kirar adidas daga ‘Pleasure Summit Restaurant’ da ke Magara Road, Iyaganku, Ibadan.

Mr Ibrahim ya kuma shaida wa kotun cewa wanda aka yanke wa hukuncin ya saci talabijin mai fadin inci 42 da kudinsa ya kai N200,000.

Ya ce laifukan sun saba wa sashi na 390(9) na kundin dokokin masu laifi na Jihar Oyo ta shekarar 2000, kamar yadda NAN ta rahoto.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button