Yan Najeriya ne suka matsa sai dai Buhari ya yi takarar shugaban kasa – in ji Garba Shehu

Abuja – Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin watsa labarai, Garba Shehu, ya ce yan Najeriya ne suka matsawa Shugaba Muhammadu Buhari don ya tsaya takarar shugaban kasa.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Shehu na martani ne ga wasu kalamai da shugaban kasar ya yi kan shirya-shiryensa kan zaben shugaban kasa na 2023.

Buhari
Yan Najeriya ne suka matsa sai dai Buhari ya yi takarar shugaban kasa, in ji Garba Shehu Hoto: Femi Adesina Source: Facebook

Buhari, a wata hira da aka watsa a tashar NTA a ranar Alhamis, 6 ga watan Janairu, ya ce ya yi iya bakin kokarinsa ga Najeriya, inda yace yana duba ga lokacin da zai huta bayan barin kujerar mulki a 2023.

Shugaban kasar ya ce:

“Game da shekaru na, ina ganin sa’o’i na, yanzu suna hutawa ne, kuma ina tabbatar maka nima ina fatan ganin bayan watanni 17 nan gaba da zan samu in ɗan huta.

“Tsufa ya fara kama ni, aiki na awa shida, bakwai ko takwas kullum a ofis ba abu bane mai sauki a yanzu; akwai batun taron majalisar koli, da takardu daga jihohi daban-daban kusan ko wane mako. Gaskiya aiki ne mai wahala, amma kaman yadda na faɗa, ni na nemi aikin don haka ba zan koka ba.

“Na yi gwamna, na yi minista, kuma ga shi ina wa’adi na na biyu a matsayin shugaban kasa. Don, haka na zaga a aikin, don haka mai kuma ya rage in yi wa kasar? Na yi iya kokari na.”

Da yake martani, Shehu wanda ya bayyana a shirin Channels TV na Sunrise Daily a ranar Juma’a, 7 ga watan Janairu, ya ce shugaban kasar ya yi daidai da ya ce ya yi iyakan kokarinsa da kasar, Sahara Reporters ta rahoto.

Shehu ya ce:

“Shugaban kasar ya kan kasance mutum mai sauki sosai wasu lokutan wajen yin magana da kuma raha; ina ganin wannan shine abun da mutane suka gaza fahimta game da shi. Ya kamata su fahimci yadda aka lallashe shi da kuma matsa masa don ya yi takara a karon farko.

“Ya yi aiki a matsayin gwamna, minista da kuma shugaban kasa a mulkin soja kuma wannan shine matsayi mafi girma da zai iya kaiwa. Ya yi ritaya ya koma gida sannan yan Najeriya suka zo suka ce kaine mutumin da ya dace a wannan lokaci, muna bukatarka. Sai da aka yi lallashi.

“Don haka, eh, daidai ne ga mutumin ya ce ya yi iya bakin kokarinsa kuma lokaci yayi, wasu mutanen za su daura daga inda ya tsaya.”

Source: Legit Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button