Sai dana fara sana’ar gwan-gwan da yaron karan mota sannan na shiga masana’antar kannywood, cewar Tijjani abdullahi asase

Sai dana fara sana'ar gwan-gwan da yaron karan mota sannan na shiga masana'antar kannywood, cewar Tijjani abdullahi asase

Shahararran jarumin wasan kwai-kwayo na masana’antar kannywood wanda shine yake jagorantar shirin nan mai dogon zango wato, Aduniya, jarumi Tijjani abdullahi asase yace: Ya fara naiman kudi ne da sana’ar gwan-gwan, sannan kuma ya kara da cewa sai da yayi karen mota kamin ya shiga masana’antar kannywood.

Jarumi Tijjani asase ya bayyana haka ne a zantawar da sukayi da Freedom Radio inda yake cewa: Babban abin da yake bigeshi a rayuwa shine yaga matashi ya rike sana’a komai kankantar ta sannan kuma ya kasance mai gaskiya da rikon amana.

Kamar yadda kowa ya sani Tijjani asase ficaccan jarumi ne a masana’antar kannywood wanda yake burge al’umma masu kallon shirin, inda yake taka rawa a roll din da yake fitowa a matsayin dan fashi ko kuma mai aikata manya manyan laifuka.

A cewar jarumi Tijjani asase: Babban abin da yake yanyo aikata manyan laifuka kama daga, kwacen waya, sata a cikin gida da dai sauransu, rashin aiki ne da wasu matasan basu samu ba sannan kuma suke raina kananan sana’o’i suke musu kallon banza, suna ganin kamar bazasu sami komai ba idan sukayi wannan sana’ar.

Haka kuma jarumin yayi fatan masana’antar kannywood taci gaba da shirya fina-finan da zasu sauya rayuwar al’umma gaba daya.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button