News

Allah Ya Kawo Ranar Da Yan Nigeria Zasu Gane Shugaban Kasa Buhari Akan Dai Dai Yake – Hassan

Daga: Fahad Kabir Maitata

Mutane mantawa suke yi, domin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sami mulki ne cikin tsarin Dumukuradiyya, wanda ba iri daya ne da mulkin Soji ba wanda zaka iya yin komai da kanka.

A wannan tsarin duk abunda zaiyi sai yakai majalissa ta sahale, wanda idan basu so ba ba lalaine ayi ba.

Malam Hassan, dattijo wanda mazaunin garin Kano ne shine ya baiyana hakan cikin tattaunawarsa da jaridaralkIblah a yammacin ranar Talata.

Ya kara da cewa an baiwa shugaban kasa mulki a dai dai lokacin da ake fama da Boko Haram, ga Rigimar Yan Biafara, ga masu zagwon kasa marasa amana acikin gwamnatin, dan haka dole za’a yimasa uziri.

“Mu da muke cikin gari, mune mukasan irin bala’in da muka gani da bamu taba ganin irinsa ba na masallacin sarki”

“Akwai masu iyayen gida agefe wanda suke cikin gwamnatin Buhari kuma suke cimata dunduniya, sune kuma suka hana ruwa gudu a kokarin magance matsalolin da ake fama dasu” acewar Malam Hassan.

Ya kara da cewa “nauyinsu ake dauka suke shuka tsayar da suke so domin al’umma su shiga mawuyacin hali ace Buhari ne, kullum fama yake dasu”

Daga karshe ya ce, duk wanda shugaban kasa ya bawa wani aiki ko mukami to yarda ce tasa, idan mutum yayi mai kyau dan kansa, bazai takura maka ba domin ya yarda da kai, wanda hakan koyi da Sunnah yake yi.

“Allah ya kawo randa Yan Nigeria zasu gane cewa shugaban kasa akan dai dai yake, kuma Allah ya kara Mai lafiya yasa ya gama lafiya” addu’ar da Hassan ya kulle da ita kenan.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button