Ni Yar Fim ce, Yar Nanaye Kuma ina Alfahari da hakan Wanda duk yaji Haushi shiya sani – Inji Maryam Booth

Tun daga shekaran jiya da akayi hira da ladin chima watau baba tambaya har izuwa yau Masana’antar Kannywood ta zama wani abin magana da kowa keta tofan albarkacin bakin sa.

Abun ma yakoma kamar gaba inda jaruman suketa martani wasu ma harda zage zage akan wannan al’amari, bayan hirar da bbc tayi da ladin chima, daga karshe tsohuwar ta bayyana cewa bbc hausa basuyi mata adalci ba.

Bayan maganarta da tayi kan cewa ba’a taba biyanta kudi masu kauri a harkar fim ba, ta kumayi godiya da jinjina ga wasu jaruman Kannywood da suke kyautata mata.

Wannan magana dai itace silar da tasa har mawaki naziru ya fito yayi rantsuwa da Allah kan cewa tanada gaskiya kuma akwai wasu Abubuwa na rashin dacewa da akeyi a Masana’antar amma anki afito a fadi gaskia

Hakan yasa Jaruma maryam booth itama wallafa wani rubutu a shafinta na Instagram inda ta bayyana cewa ni yar fim ce yar drama, yar nanaye, kamar yadda kuke kiranmu Kuma ina alfahari da hakan.

sannan ina alfahari da kowa a Masana’antata wannan shine abinda nake son ku gane, Abu na biyu kuma shine don Allah idan mutum zaiyi Zargi akan wani abu to ya dinga bada misali akan wane da wane domin a gane.

Ta kara da cewa idan har wani ko wata yanason yayi magana akan rayuwata kamar dai misalin abinda yake faruwa a yanzu to abin tambayar anan shine kai waye da zaka hukuntani?

Rayuwata tawa ce kamar yadda bani da iko akan taka, amma idan har kukaci gaba da damuwa da matsalolina to wannan kuta shafa.

Idan akwai wanda yake ganin cewa Masana’antar bata tafiya yadda yakamata to yazo yasa Kudinshi koya shigo ya gyara, a karshe kuma bana tare da maganar da sarkin waka ya fada na cewa ana lalata da mata kafin asakasu acikin fim.

Ga Vedion nan a kasa

Source: KaiTaTunes

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button