Mutunm 6 Sun Sha Da Kyar A Hatsarin Jirgin ’Yan Sanda A Bauchi

Mutum shida sun tsallake rijiya da baya a sakamakon hatsarin wani helikwaftan ’yan sanda a Jihar Bauchi.
Jirgin ’yan sandan ya yi hatsari ne a ranar Laraba amma ba a samu asarar rai ba, amma duk mutum shidan da ke cikinsa sun samu rauni, kamar yadda Aminiya ta gano.
Hukumar Binciken Hatsarin Jiragen Sama ta ce helikwaftan da ya taso daga Abuja, dauke da mutum shida ya yi hatsari ne da misalin karfe 7:30 na dare ranar Laraba a filin jirgin saman da ke jihar.