Kotu Ta Tura Danbilki Kwamanda A Gidan Yari Kan Bata Sunan Ganduje

Wata kotun majistare da ke zamanta a unguwar Nomansland a Kano to aike da dan siyasar nan da ya yi kaurin suna wajen sukar gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje a kafafen yada labarai, Abdulmajid Danbilki Kwamanda, gidan gyaran hali.

Alkalin kotun mai lamba takwas, Mai Shari’a Aminu Gabari ne ya ba da umarnin yayin zaman kotun a ranar Talata.

Hakan ya biyo bayan yin watsi da bukatar lauyoyin Danbilki Kwamanda kan ba da belinsa.

An dai gurfanar da Kwamanda ne bisa laifuka uku, masu jibi da bata sunan Ganduje, inda ya zargi Gwamnan da cin hanci ga shugabancin riko na APC na kasa da ke karkashin jagorancin Mai Mala Buni, don tsaginsa ya karbi takardar zama halastaccen shugabancin jam’iyyar a Jihar Kano.

Alkalin dai ya aike da shi gidan kason ne bayan ya ki amincewa da bukatar lauyoyinsa kan bayar da shi beli.

Sai dai wanda wanda ake zargin ya musanta aikata laifukan da ake zarginsa da su.

Daga nan ne alkalin ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa 15 ga watan Maris din 2022, tare da umarnin ci gaba da tsare shi a kurkuku har zuwa lokacin.

Danbilki Kwamanda dai tsawon lokaci ya yi kaurin suna wajen sukar lamirin Ganduje a akasarin shirye-shiryensa a gidajen rediyon da ke ciki da wajen Jihar.

Sai dai ba shi ne mai sukar Gwamnan na farko da aka taba tsarewa a kurkuku ba.

Idan za a iya tunawa, ko a watan Janairun 2022 da ya gabata, sai da aka tsare tsohon Kwamishina a gwamnatin Gandujen, Injiniya Mu’azu Magaji saboda zargin aikata makamancin wannan laifin, har sai da ya cika sharudan belin nasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button