Boko Haram: Harin Bom Ya Hallaka Jami’an Tsaro 7 A Neja

Wasu bama-bamai da ake zaton mayakan Kungiyar Boko Haram ne suka binne sun tashi da wasu jami’an tsaro na Civil Defence inda bakwai suka riga mu gidan gaskiya.

Rahotanni sun bayyana cewa mayakan sun binne bama baman ne a kan hanyar zuwa garin Galadiman Kogo ta yankin Karamar Hukumar Shiroro a Jihar Neja.

Jami’an na Civil Defence sun taka daya daga cikin bama-baman ne a kan hanyarsu ta kai dauki garin na Galidaman Kogo a yayin da ’yan bindiga suka kai hari a ranar Lahadi.

A hirar shi da Muryar Amurka, wani mazaunin garin Erana mai iyaka da yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya yi karin bayani ta wayar salula inda ya bayyana yadda lamarin ya faru.

A cewar Erina, “Sun zo ne suka dinga banka wa gidaje wuta tare da dasa bama-bamai a cikin gari, akwai motar civil defense daya ma da ya taka bam din har ya tarwatsa motar.”

Duk da ya ke kokarin jin tabakin jami’an na Civil Defence a Jihar Nejan ya ci tura , sai dai rundunar ’yan sanda ta Jihar Nejan ta tabbatar da aukuwar lamarin.

A bayaninsa, Monday Bala Kuryas Kwamishinan ’yan sandan Jihar Neja, ya ce yanzu haka ’yan sanda masu aiki da bama-bamai za su je su ga yadda za su cire sauran bama-baman.

Kawo lokacin hada wannan rahoto dai babu wani karin haske a hukumance daga bangaren gwamnatin Jihar Neja.

Wannan hari na bom dai tamkar wata alama ce dake nuna cewa mayakan Boko Haram sun mamaye madatsar ruwan na shiroro daya daga cikin tashoshi 3 dake samar da hasken lantarki a Najeriya.

A ranar Litinin ce dai Aminiya ta ruwaito cewa ana zargin ’yan bindiga ne suka kai hari inda kawo yanzu ba a tabbatar da adadin mutanen da suka rasa rayukansu ba.

Wani Shugaban Kungiyar Matasan Shiroro mai suna Sani Abubakar, ya shaida wa manema labarai cewa akwai yiwuwar mutane da dama sun halaka a harin na abin fashewa da bakon abu ne a yankin.

Ya ce: “Mutane sun shiga cikin matsanciyar damuwa a yankunan da yan ta’adda ke yawan kai hari saboda tashin abin fashewar da ya auku.

“Fashewar Bam ko wani abu makamancin haka sabon abu ne a yankunan kuma bai saba faruwa ba, sai dai za mu alakanta haka da irin rikon sakainar kashi da gwamnati ta yi wa matsalar tsaro a Jihar.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button