An Kama Karamin Yaro Da Turji Ke Amfani Da Shi Ya Kai Hari

An kama wani karamin yaro mai shekara 14 wanda jagoran ’yan bindigar Jihar Zamfara, Bello Turji, yake amfani da shi wajen kai wa al’ummomi hari.

Bayan an kama dan aiken na Turji, ya shaida wa jami’an tsaro cewa Turji ya ba shi horo kan yadda ake sarrafa bindigogi iri-iri.

Ya kuma bayyana wa jami’an tsaro cewa Bello Turji yakan yi amfani da wajen dana tarko domin kai wa al’ummomi hare-hare da kuma yin garkuwa da mutane.

Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC), ce ta cafke dan aiken na Turji a wani samame da ta kai a Jihar Zmafara.

Kakakin NSCDC a Jihar Zamfara, Ikor Oche, ya ce yaron ya shaida musu cewa yakan yi amfani da raunin matan da gungunsu suka yi garkuwa da su, yana yin lalata da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button