Africa Initiative for Governance (AIG) Scholarships 2022/2023
Ofishin babban mukaddashin Gwamnatin tarayya na sanar da daukacin zakwakuran ma’aikatan gwamnati wata dama ta scholarship a babbar jamai’ar kasar England wato Oxford University mai lakabi da Africa Initiative For Governance wadda Aig-Imoukhuede foundation ke aiwatarwa a matakin Master of public Policy (MPP) degree.
Za’a bawa wanda yayi nasarar samun wannan scholarship zunzurutun kudin England har pound 50,000. A wannan shekara za’a bawa wadanda ke aiki a gwamnati ne kawai. Sannan wadanda zasu nemi wannan schoalship shekaraunsu yazama daga 25 zuwa 50 sannan su zamo suna da fikira da kwarewa ta aikin da sukeyi.
Gwamnatin tarayya ta bude neman wannan scholarship ne a ranar 20th September 2021 a inda za’a rufe a 10th October 2021, sai final selection a December 2021.
Domin cike wannan gagarumar dama sai a ziyarci wannan link: Apply Now