Kano Science and Technical Board Ta Sanya Ranar Fara Sayar da Scratch Card 2022
Hukumar ta Kano Science and Technical Board ta sanar da ranar da zata fara sayar da katin dake bada dama wajen yiwa sababbin Ɗalibi rijista domin samun gurbin karatu na shekarar 2022.
Kamar yadda aka saba a kowace shekara Ɗalibai masu tarin yawa su kan nemi gurbin karatun a wannan makarantu duba da yadda suke da ƙokari da kuma horar da Ɗalibai yadda ya kamata a fannin kimiya da fasaha.
Kamar yadda wakilin Arewatalent ya zanta da wani Jami’I na Board din yace “Za’a fara sayar da Scratch Card din a ranar Litinin” 4th April 2022 makon gobe.
Da zarar an fara sayarwa zamu sanar da al’umma inda zasuje domin yin rijstar akan lokaci domin gujewa zuwa wajen ƃata gari.
Kafin lokacin yin rijistar a tabbata dukkan bayanan Ɗalibai babu wata matsala musamman wajen shekarar haihuwa da yadda jerin suna yake a rubuce.
An kafa ita wannan hukuma ta science schools management Board a shekarar 1977 domin samar da gwarazan dalibai a fannin kimiya da fasaha domin ciyar kano gaba dama kasa bakidaya.
Wannan board ta fara ne da makarantu guda biyu kamar haka:
1. Science Secondary School Dawakin Tofa
2. Science Secondary School Dawakin kudu
A yanzu haka akawai kimanin makarantu 38 a karkashin wannan hukuma kamar haka:
1. Akwai Boarding Boys Schools guda 10
2. Akwai Day Girls schools guda 10
3. Akwai Boarding Girls guda 10
4. Akwai Day Technical schools guda 10