NewsNigeria

‘Ya kamata a kara wa’adin daina karbar tsoffin takardun kudi a Najeriya’

Yayin da wa’adin daina amfani da tsoffin takardun kudin Najeriya da Babban Bankin kasar ya diba ya kusa zuwa karshe, wasu jagororin al’umma sun yi kira ga bankin da ya dubi lamarin da idon rahama a kara lokaci.

Duk da cewa masu ruwa da tsaki sun tattauna lamarin a baya, har yanzu dai da sauran rina a kaba kan wannan lamari na sauya kudaden kasar, saboda wasu al’ummar Najeriyar musamman mutanen karkara na cikin damuwa.

 

Daya daga cikin jagororin al’ummar da ya yi wannan kira shi ne gwamnan jihar Yobe da ke arewa maso gabashin kasar Mai Mala Buni.

Mai magana da yawun gwamnan, Mamman Muhammed, ya shaida wa BBC cewa, gwamnan na da bukata ta musamman ga Babban Bankin na Najeriya, saboda a jihar ta Yobe, kananan hukumomi hudu ne kadai ke da bankuna.

Ya ce “Kananan hukumomin jihar 13 ba su da bankuna, don haka kayyade wannan lokaci na daina amfani da tsoffin takardun kudi, ba zai ba wa  mutanen da ke zaune a kananan hukumomin da basu da bankuna damar mayar da tsoffin kudin da ke hannunsu ba.“

Wannan dalili ne ya sa gwamnan na Yobe ya bukaci Babban Bankin Najeriyar CBN, da ya kara wa’adin daina karbar tsoffin kudin, ko al’ummar jiharsa sa samu su mayar da kudaden hannunsu musamma mazauna karkara, in ji mai magana da yawun gwamnan.

Mamman Muhammed, ya ce gwamnan na Yobe, Mai Mala Buni, ya kuma bukaci CBN din da ya samar wa jiharsa da wani tsari ta yadda jama’a za su samu su canja kudinsu.

A jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ma, mai ba wa gwamnan jihar shawara a kan al’amuran da suka shafi harkokin waje da yarjeniyoyi, Hon. Dakta Suleiman Shehu Shinkafi, tsokaci ya yi a kan yadda kayyade lokacin da CBN din ya yi ya shafi al’ummar Shinkafi.

Ya ce, babbar matsalar da ake fuskanta a yanzu itace idan mutanen karkara sun shiga karamar hukumar Shinkafi sun je banki sun kai kudi ba a karba, haka ma idan suka je sayen wani a kasuwa, to ‚yan kasuwar basa karbar tsoffin kudi.

Dakta Suleiman Shehu Shinkafi, ya ce bankuna a Shinkafi sun fara daina karbar tsoffin kudi alhali shi kansa CBN, bai ce a daina ba tukunna.

Ya ce, ‚‘‘ Sai mutane sun bayar da wani abu sannan za a karbi kudinsu a banki a Shinkafi, don haka mu ba mu gane ba, su kansu sabbin kudin da aka ce sun fito mu bamu gansu ba, to idan an ce ba za a karbi tsoffin kudi ba to kuwa yunwa duk sai ta kashe mu.“

Mai ba wa gwamnan na Zamfara shawara, ya ce su abin da suke so shi ne CBN, ya tabbatar da cewa an sanar da bankunan da ke kauyuka musamman na Shinkafi da su rinka karbar tsoffin takardun kudi ba tare da an bayar da ko sisi ba, tun da ai wa’adin bai cika ba tukunna ba.

Kwanaki kalilan ne dai suka rage a daina amfani da tsoffin takardun kudi a Najeriya kamar yadda Babban Bankin kasar ya sanar.

A ranar Laraba 26 ga watan Oktoba ne Babban Bankin Najeriyar ya sanar da matakin sauya fasalin kudin kasar daga takardar naira 200 zuwa 1000, inda ya buƙaci masu kuɗi a hannu su mayar da su bankuna cikin ƙasa da kwana 50. 

Dama CBN din, ya ce sabbin kudaden da aka samar za su fara yawo a hannun mutane daga ranar 15 ga watan Disambar 2022, sannan kuma za a ci gaba da amfani da tsofaffin kudaden har nan da ranar 31 ga watan Janairun 2023. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button