Jami’in Tsaro Ya Kashe Dan Tireda Saboda Karan Sigari A Kano

Wani jami’in tsaron gidan yari ya harbe dan tireda har lahira saboda karan taba sigari a Jihar Kano.

Jami’in da ba a bayyana sunansa ba, ya bude wa dan tiredan wuta ne saboda ya ki sayar mishi da sigari a ranar Litinin.

Ganau sun shaida wa Aminiya cewa, “Da alama bashi dan tiredan yake bin jami’in, da ya zo zai kara karba a wannan karon kuma dan tiredan ya ki ya ba shi.

“Wannan ne ya fusata jami’in tsaron gidan yarin ya harbe shi.”

Shaidu sun ce harsashin da aka harbi mai shagon ya fasa cikinsa ya kuma sami wani mutum a kafa, a rikicin.

Sun shaida wa wakilinmu cewa an garzaya da wadanda aka harba din Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano inda likitoci suka tabbatar cewa mai shagon ya rasu.

Da yake bayani game da abin da ya faru, Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce suna gudanar da bincike don gano asalin wanda aka kashe din.

Wakilinmu ya nemi samun karin bayani daga mai magana da gidan yarin, Musbahu K/Nasarawa, amma ya ce zai neme shi daga baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button