Masu cewa ba ni da isasshen lafiya basu da hankali, mahaukata ne: Tinubu

Jigon jam’iyyar All Progressives Congress APC kuma dan takaran kujeran shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa mutum mai hikima da kwazo ake bukata matsayin shugaba ba lebura ko maji karfi ba.

A kalamansa, aikin shugaban kasa ba na hawa kan tsauni bane ko diban kankare, aikinsa tunani da amfani da kwakwalwarsa.

Yace:

“Ba dan damben WWE ake bukata ba, mai tunani kan yadda za’a samar da tsaro, wanda zai yi nazari kan lamuran tattalin arziki kuma ya inganta ake bukata.”

Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a Minna, yayinda ya tafi yawan kamfe wajen deleget na APC a jihar, rahoton Punch.

Tsohon gwamnan na Legas ya bayyanawa deleget din cewa masu zaginsa bisa rashin lafiyan da yayi basu da hankali irin nasa.

Yace:

“Basu da irin kwakwalwata amma suna zagi na kullun, ‘wai bai da lafiya, kafarsa na ciwo,…babu mai kwalin asibitin da nike da shi cikinsu.”

“Basu da hankali ko kadan kuma basu da wani abin fadi da ya wuce zagi na amma na rabu da su.”

Tinubu ya kara da cewa ya sauya fasalin jihar Legas kuma ya gyarata, haka yake son yiwa Najeriya.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button