Pogba Zai Zama Dan Wasa Mafi Albashi A Tarihin Firimiya

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta yi wa Paul Pogba tayin biyansa fan 500,000 duk mako domin shawo kan dan wasan na Faransa ya ci gaba da zama a kungiyar.

Kafofin watsa labaran wasanni da dama sun ruwaito cewa idan har Pogba ya amince da sabon albashin, zai kafa tarihin zama dan wasa mafi yawan albashi a gasar Firimiyar Ingila.

Sabon tsarin albashin da aka gabatar wa Pogba ya zarce abin da tauraron kulob din na United Cristiano Ronaldo ke samu duk mako.

Cristiano Ronaldo ya zama wanda ya fi kowa karbar albashi a United inda ake biyansa fam dubu 400,000 duk a mako, bayan komawarsa kungiyar daga Juventus a bazarar da ta gabata.

Yanzu haka dai Pogba na cikin watanni shida na karshe a yarjejeniyarsa da Manchester United bayan da ya ki amincewa da tattaunawa kan tsawaita zamansa a kungiyar.

Kungiyoyin Real Madrid da Paris Saint-Germain da Juventus ne kungiyoyin da ke kan gaba a Turai wajen fatan sayen dan wasan na Faransa kafin ko kuma a lokacin sabuwar kakar wasanni.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button