Producer Alhaji Sheshe ya yiwa jaruma Hadiza gabon da kawali zazzafan martani

Producer Alhaji Sheshe ya yiwa jaruma Hadiza gabon da kawali zazzafan martani

Idan bazaku manta ba mun kawo muku labarin yadda jaruma Hadiza gabon da wasu jarumai a masana’antar kannywood suke ganin shishigi ne yasa jarumi Ali nuhu da wasu mutane a kannywood suka halarci wajan shagalin bikin Big brother inda har suka dauki hotuna a wajan.

Wanda a yanzu shima yayi martani kamar haka:

producer Alhaji SHESHE tare daba daya daga cikin mutanen da suka shiga gidan Big brother wato Whitemoney dan asalin jihar Kano ne kuma ya sami lambar yabo a wajan mu wajan yadda ya girmama kannywood da mutanen cikinta.

Dalilin da yasa naga ya birgeni kenan sabida ya nuna mushimmancin masana’antar shirya fina-fina ta Hausa da kuma yadda ya nuna jaruman fim din hausa suna birgeshi har yayi misali da daya daga cikin jaruman mu a wata shira da yayi a cikin gidan Big brother.

Haka yasa bayan fitowar su daga gidan sai shugaban gidan Talabijin na African Music suka shirya wata mushimmiyar ganawa da masu ruwa da tsaki na masana’antar kannywood tare da shi wannan mutumin da yazo na daya a gidan Big brother domin nunawa duniya mushimmancin masana’antar kannywood da kuma kulla alakar cigaba da chinikayya a tsakanin mu.

Babban abin da yafi bani mamakin da naga wasu mutane daga cikin masana’antar kannywood suna cewa munyi shishigi wasu kuma suna cewa anyi hoto basu saka a page din su ba.

To dama an fada muku munyi hoto ne don su dora a page din su mutanen nan fa zuwa sukayi su gaishe mu suka kuma girmama mu sannan suka girmama masana’antar mu suka kuma kara bamu hadin kai domin muci gaba da cinikayya a tsakanin mu da su.

A cikin magangannun ku a nau’i na rashin sanin mushimmancin sana’ar fim sannan akwai nau’i na hassada akwai kuma nau’i na rashin sanin mushimmancin daukaka banyi mamaki ba ganin yadda wani kawali yayi rubutu dama ai mun san ba sana’ace ta kawo shi kannywood ba ka fake da ita ne kana diban ‘yayan mutane kana hada su da iyayan gidan ka fasikai kana kashe aure kana cin amanar mutane da sukai maka sutura kana zagin mutanen da suka kyautata maka.

Allah ka rabamu da yin magana akan abin da bamu da masaniya a kai.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button