Majalisar Zartarwa Ta Amince Da Ƙarin Albashi Ga Jami’an Ƴan Sanda

Daga: Nura Ahmad Hassan

Majalisar zartarwa ta tarayya, ta amince da karin kashi 20 cikin 100 na albashin jami’an ‘yan sanda daga watan Janairun shekarar 2022.

Ministan harkokin ‘yan sanda, Maigari Dingyadi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa a karshen taron majalisar zartaswa, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa ta Villa, a Abuja.

Ministan ya bayyana cewa karin albashin jami’an ‘yan sandan da kashi 20 cikin 100 a halin yanzu na daya daga cikin hanyoyin inganta alaka tsakanin rundunar da al’ummar Najeriya.

Majalisar ta kuma amince da sake duba alawus-alawus na ’yan sanda na yawon shakatawa da alawus-alawus zuwa kashi shida cikin 100, da kuma sakin Naira biliyan 1.2 domin biyan alawus-alawus da kuma ba su inshora.

Haka kuma, ya ce majalisar zartaswa ta amince da kashe Naira biliyan 1.2 don biyan wasu alawus-alawus. Amincewar ya yi daidai da alkawarin da shugaba Buhari ya yi na inganta albashin ‘yan sanda kamar yadda masu zanga-zangar #EndSARS suka bukata.

Ministan ya ce an amince da kudi Naira biliyan 13.128 don samun tallafawa wadan da suka rasu na ‘yan sanda 5,472.

Sai dai ya ce za a fara biyan kudin ne bayan babban mai binciken kudi na tarayya ya binciki lamarin. Sannan ya sanar da rage harajin Naira biliyan 18.6 daga tsakanin mataki na daya zuwa mataki na 14.

Sai dai Ministar Kudi, Kasafin da tsare-tsare na Kasa, Zainab Shamsuna Ahmed ta ce karin albashin ‘yan sanda ba a saka shi a cikin kudirin kasafin kudin shekarar 2022 ba. Amma gwamnati za ta iya kara wani abu a cikin kasafin kudin a aika da shi Majalisar Dokokin kasa domin amincewa da shi.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button