Allah Ya Yi Wa Janar Mohammed Wushishi Rasuwa

Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Janar Mohammed Inuwa Wushishi ya riga mu gidan gaskiya.

Related Articles

Iyalan marigayin sun ce ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Landan na kasar Birtaniya yana da shekara 81.

Janar Wushishi ya kasance Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya a Jamhuriya ta biyu, daga 1981 zuwa 1983.

An haife marigayi Janar Wushishi ne a shekarar 1940 a garin Wushishi, hedikwatar Karamar Hukumar Wushishi ta Jihar Neja.

A tsawon rayuwarsa ta aikin soji, ya rike mukamai da dama ciki har da Kwamandan Kwalejin Horon Shugabancin Soji (CSC) da ke Jaji a Jihar Kaduna da kuma Babban Kwamandan Runduna ta 4 na Mayakan Kasa na Sojin Najeriya.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button