An Sake Kama Wasu Fursunonin Bayan Sun Tsere Daga Gidan Gyaran Hali

Daga: Nura Ahmad Hassan

Related Articles

Rundunar ‘yan sandan jihar Plateau ta ce ta sake kama wasu fursunoni bakwai da suka tsere daga gidan gyaran hali da ke Jos.

Ubah Ogaba, wanda shi ne jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ya tabbatar da sake kama fursunonin a wata sanarwa.

Ya bayyana cewa kwamishinan ‘yan sanda na jihar Plateau Bartholomew Onyeka ne ya jagoranci wasu ma’aikata da suka kai farmaki wurin da lamarin ya faru, a killace yankin baki daya, biyo bayan rahotannin da aka samu cewa wasu ‘yan bindiga sun kai wa gidan gyaran hali hari, lamarin da ya kai ga tserewar wasu fursunoni a wurin.

A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan, nan take ‘yan sandan suka fara gudanar da bincike inda suka sake kama wasu mutane bakwai da suka tsere. Yayin da fursunonin da aka sake kama suka tsare, an ce wani da ya tsere daga gidan ya mika kansa ga ‘yan sanda bisa radin kansa. Wannan sakamako bisa daukin gaggawar da aka kai kan harin, an shawo kan lamarin sakamakon harbi da manyan bindigogi da jami’an tsaro suka yi a wurin.

Jaridaralkiblah ta rawaito cewa wannan kame ya biyo bayan harin da wasu gungun ‘yan bindiga da ba a tantance ko su wanene ba suka kai wa ginin gidan gyaran halin da ke babban birnin jihar a ranar Lahadi.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button