Kano: Wani DPO Yazo Na 1 A Gasar Karatun Qur’ani

Daga: Fahad Kabir Maitata

Wani DPO mai suna Mahi Ahmed Ali wanda yake a o’fishin Yan sanda na karamar hukumar Takai a jihar Kano shine ya lashe gasar karatun Qur’ani da aka fara tun jiya Laraba.

Gasar wadda ta kunshi kusan dukkan masu mukami na jami’an an yita mataki bayan mataki, daga Izu 60 zuwa 40 zuwa 5 da kuma 2.

Yanzu haka dai DPO Mahi ya Fara karbar kyautuka daban daban bayan zuwan sa na 1 a gasar, an kuma sami halattar mahaddata Qur’ani da gwanaye a wajan domin tantancewa.

An dai gudanar da taron musabakar a shelkwatar rundunar Yan sanda ta jihar Kano dake a Bompai karkashin jagorancin kwamishina CP Sama’ila Sha’aibu Dikko.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button