SSS sun kame matashin da ya zolayi Zainab Nasir kan auren ‘yar gwagwarmaya Malala

Kano – Hukumar tsaron farin kaya ta SSS a Kano ta kama wani mai amfani da kafar Facebook, Ibrahim Sarki Abdullahi, da laifin zolayar wata mai fafutukar kare hakkin mata, Zainab Nasir kan auren ‘yar fafatuka Malala.

Wata majiya a ofishin hukumar ta Kano ta tabbatar wa Daily Nigerian kama Mista Abdullahi, inda ta ce ana yi masa tambayoyi ne saboda taba mutuncin Zainab.

A baya dai Zainab ta bayyana ra’ayin cewa “aure ba nasara ba ne”, kuma hakan ya haifar da cece-kuce a kafar Facebook, lamarin da yasa ta shahara.

Abdullahi ya zolayi Zainab ne a ranar da Malala Yousafzai ta bayyana auren ta ga duniya, wanda hakan ya haifar da rudani duba da ra’ayin Malala kan batun sukar aure.

Maganganun Abdullahi sun danganta Zainab da Malala ne ganin suna da ra’ayi iri daya, a hasashen Abdullahi.

A cikin rubutunsa, Abdullahi ya sanya hoton Zainab tare da zolayar da cewa “Malala ta shushe mu”.

Daga nan Zainab tace ba za ta amince ba sai ta dauki matakin doka bayan shawarwari.

Sai dai, jim kadan rahoton kame Abdullahi da yi masa tambayoyi, an ga rubutu a kan shafinsa na Facebook, inda ya ce:

“SalamuAlaykum.”

Legit.ng Hausa ta bibiyi rubutun, amma har zuwa lokacin hada wannan rahoton bai yi karin bayani an sako shi ko musanta kamun ba.

Haka zalika, mabiyansa a shafin Facebook sun yi ta tambayoyi kan batun.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button