Borno: Hotunan ragargazar da sojoji suka yi wa ISWAP a Askira Uba, sun kashe 50 sun kwato makamai

Rundunar Operation Hadin Kai ta ragargaji mayakan ISWAP 50 sannan ta lalata musu makamansu da ke sansaninsu a karamar hukumar Askira Uba da ke jihar Borno.

Idan ba a manta ba bataliyar 115 Task Force ta yi karon batta da mayakan ISWAP a ranar 13 ga watan Nuwamban 2021 a Askira Uba.

Sai dai sakamakon turnukun, mayakan ISWAP sun halaka kwamandan 28 Task Force tare da wasu sojoji 3 har lahira, wanda hakan ya matukar harzuka sojoji

Rundunar Operation Hadin Kai ta Sojoin Nigeria da ke arewa maso gabas ta samu nasarar halaka mayakan ISWAP guda 50 a karamar hukumar Askira Uba.

Hedkwatar tsaron Najeriya ta shafin su na Facebook sun bayyana yadda sojojin su ka yi gaba da gaba da mayakan ISWAP wanda har lalata mu su kayan yakin su suka yi.

Ku kalla hotunan a kasa:

Lamarin ya auku ne a ranar Litinin, 15 ga watan Nuwamba inda jaruman sojin suka samu nasarar halaka manya da kananun mayakan kungiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button