Arsenal na neman yan wasa biyu, Paul Pogba da Kylian Mbappe sun haqura da tafiya.

Dan wasan tsakiya na Manchester United Paul Pogba, mai shekara 28, ya dawo daga rakiyar zawarcinsa da Paris St-Germain (PSG) da Real Madrid da kuma Juventus suke yi, inda yanzu zai ƙulla sabuwar yarjejeniya a Old Trafford.

Manchester City da Chelsea da Manchester United na shirin fafatawa domin ɗauke matashin ɗan wasan Ingila na ƙungiyar Stoke City Emre Tezgel, mai shekara 16, wanda ake kwatanta shi da Harry Kane.

Ƙungiyoyin gasar Premier za su bi Bayern Munich a gogayyar da take wajen dauke dan wasan tsakiya na Jamus Florian Wirtz, mai shekara 18 daga Bayer Leverkusen. (Fabrizio Romano).

Liverpool na duba yuwuwar ɗaukar dan wasan gaba na Serbia Dusan Vlahovic, yayin da tattaunawa kan kwantiragin ɗan wasan mai shekara 21 ta watse a Fiorentina.

Har yanzu Arsenal na sha’awar sayen ɗan gaban Club Bruges Noa Lang, mai shekara 22, amma kuma AC Milan ma na sonsa. (Calciomercato, daga TeamTalk)

Watakila sai Manchester United ta sayar da Nemanja Matic, mai shekara 33, ko Donny van de Beek, mai shekara 24, kafin ta samu damar sayen ɗan wasan tsakiya na West Ham Declan Rice, mai shekara 22.

Borussia Dortmund ta ƙuduri aniyar ci gaba da riƙe dan wasanta na gaba ɗan Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 21, har zuwa 2023. (Sport Bild )

A shirye Juventus take ta saurari tayi daga ƙungiyoyi a kan ɗan wasanta na tsakiya dan Wales Aaron Ramsey mai shekara 30. (Mail)

Wataƙila turaron ɗan wasan Faransa Kylian Mbappe mai shekara 22, ya ci gaba da zama a Paris St-Germain bayan da mahaifiyarsa take tattaunawa a kan ci gaba da zamansa a kungiyar na tafiya daidai.

Barcelona za ta saki ɗan bayanta na Faransa Samuel Umtiti a watan Janairu. Dan wasan mai shekara 27 bai taka wa ƙungiyar ko da minti ɗaya na wasan La Liga ba a bana. (Sport )

Abokan hamayya AC Milan da Inter Milan na kan-kan-kan wajen zawarcin dan wasan gaba na kungiyar River Plate Julian Alvarez, ɗan Argentina mai shekara 22. (CalcioMercato)

Darajar hannun jarin Manchester United ta fam miliyan 9.5 da iyalan Glazer suka sanya a kasuwar hannun jari ta New York ta ƙaru zuwa fam miliyan 15.7 saboda komawar Cristiano ƙungiyar.

SPORT NEWS BY HAUSADROP.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button