An kama wasu mutane 2 da suka hada baki da mata mai juna 2 sukayi garkuwa da ita domin su karbi kudi a hannun mijinta

An kama wasu mutane 2 da suka hada baki da mata mai juna 2 sukayi garkuwa da ita domin su karbi kudi a hannun mijinta

Wata masa mai suna Nafisa Saleh wanda take dauke da juna 2, inda Nafisa Saleh ta hada baki da wasu mutane 2 domin suyi garkuwa da ita, hakan ya faru ne a Damaturu babban birnin jihar Yobe.

Daga baya an nemi matar mai suna Nafisa Saleh an rasa ta tun ranar 1 ga watan Oktoba shekara ta 2021 akan hanyar zuwa asibitin kwararru dake Damaturu domin a mata awo na ciki.

Bayan garkuwar da mutane biyun 2 sukayi da Nafisa Saleh dama sun hada baki da ita, sai suka kira mijinta domin ya kai musu kudin fansa.

sai dai a binciken da ‘yan sanda sukayi ya tabbatar da cewa: Daga baya aka gano da hadin bakin Nafisa Saleh akayi garkuwar da ita domin ta sami kudade a hannun mijin nata da kuma ‘yan uwanta.

ASP Dungus Abdulkarim kakakin ‘yan sandan jigar ta Yobe, a wata takarda daya fitar a ranar Talata ya bayyana cewa, ‘yan sanda sunyi gaggawa wajan fara aikin nasu inda suka gano gaskiyar lamarin.

Dungus Abdulkarim ya kara da cewa: Rundunar ‘yan sandan sun kama mutanen guda 2 wanda Nafisa Saleh ta hada baki dasu sukayi garkuwa da ita, Goni Modu da Umar mai Gudusu, wanda duk ‘yan kauyen Dajinge ne dake karamar hukumar Gujba a jigar Yobe.

Bayan kama mutane biyun 2 da akayi anyi gaggawa wajan wucewa da Nafisa Saleh asibiti domin a duba lafiyarta sabida halin da aka tsinceta a ciki.

To masu sauraran mu a nan muke kawo muku karshen wannan labari, muna bukatar ku danna alamar Subscribe domin samin cigaban labaran mu a duk sanda muka wallafa mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button