ABUBUWAN DA HAILA TAKE HANAWA

Da sunan Allah mai rahma mai jinkai

Allah kai salati da salami ga mai garin madina

Bayani akan jinin haila ko jinin al’ada a saukake

KASHI NA HUDU

ABUBUWAN DA HAILA TAKE HANAWA

sun kasu kashi bakwai

  • SALLAH

Mai haila bazatayi sallaba,

Domin Annabin rahma ya ce:-Idan mace tana haila baza tayi sallaba.

Bukharine ya rawaitoshi

  • AZUMI

In mace tana haila baza tayi azumiba,

Amma  za ta ra ma bayan jinin ya dauke

Annabin rahma ya ce:-

In mace tana haila baza tayi azumiba.

Bukharine ya rawaitoshi

  • DAWAFI

In mace tana haila baza tayi dawafiba

Domin Annabin rahma yana cewa:-

Shi dawafi kamar sallane saidai shi anayin magana acikinsa

Tirmizi da daru’kudni suka rawaitoshi

Sannan Annabin rahma yana fadawa Nana Aisha kiyi duk abinda mai aikin haji yakeyi Amma banda dawafin dakin Allah

Wato mai haila zatayi komai na aikin haji in banda dawafi.

  • DAUKAR ALKUR’ANI MAI GIRMA

Mai haila bazata taba ko ta shafi alkur’aniba cikin mafi yawan maganganun malamai

Domin Allah yana cewa:-shi Alkur’ani mai girmane,babu mai shafarsa sai masu tsarki,

Sannan Annabin rahma yana cewa:-karka shafi alkur’ani sai kanada tsarki,

Amma babu laifi a buda ta karanta ko tilawa wato ta karanta abinda ta haddace daka,ba tareda ta rike alkur’aniba.

  • SHIGA MASALLACI

Mai haila bazata shiga masallaciba,saboda Annabin rahma yana cewa:-

Bazan halartawa mai haila ko janaba shiga masallaciba.

Abu dawud shine ya rawaitoshi

  • SADUWA

Mai haila mijinta bazai sadu da itaba

Saboda Allah yayi hani acikin alkur’ani

Inda yake fadawa Annabin rahma cewa:-

Suna tambayarka abisa masu haila to kace musu shi haila cutane

Ku kaucewa mata in suna haila karku kusancesu har sai sun samu tsarki.

Kuma har sai sunyi wankama za’a sadu dasu

Sannan Annabin rahma yana cewa:-kar a sadu da mata harsai sun samu tsarki.

Amma babu laifi ayi wasa dasu indai ba saduwa akayiba

Saboda Annabin rahma yana cewa:-ku aikata komai(da mata)in banda saduwa.

  • SAKI

Baza’a sakin maceba in tana haila,

saboda wata rana Sayyidi Abdullahi dan Saiyidi Umar Allah ya kara musu yarda,

Ya saki matarsa tana haila sai Annabin rahma ya bada umarni a dawo da ita in yaga dama bayan ta gama hailar ya saketa ko ya rike matarsa

Amma malamai sunce koda mutum ya saki matarsa tana haila to sakin ya zartu wato ta saku.

Godiya ta tabbata ga Allah

Mu hadu a kashi na biyar in Allah ya yarda

ABU MADINA

ALI AUWAL ZAGE KANO

Dan Karin bayani 08067238367.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button