Kannywood

‘Duk Wanda Ya Kara Sa Jarumar Da Ta Fito Daga Gidan Mijinta A Fim Wuta Balbal’

Furodusa kuma mai wasan barkwanci na masana’antar Kannywood, Malam Habu wanda aka fi sani da Mazaje, ya yi kira da a daina sa duk wata jarumar masana’antar da ta yi aure, sannan aurenta ya mutu ta dawo masana’antar.

A wani dan karamin bidiyo da ya fitar, Mazaje ya ce, “duk wani furodusa ya sake wata ta fito a aure ya saka ta a fim, ni babu abin da zan ce masa, sai wuta balbal.

Sannan ya rubuta a saman bidiyon cewa, “duk wata jarumar Kannywood da ta yi
aure ta fito aka sata a film, wuta balbal.”

Sai dai wani mai suna Imrana CMC ya mayar masa da martani, inda ya ce, “to kai a su wa a Kannywood? Kai da dan wasan barkwanci ne. Mazaje ba ka iya magana ba, watarana bakinka shi zai jawo a daure ka. Ka bi a hankali.”

Mazaje shi ne forodusan fim xin ‘Daga wasa’ mai dogon zango da yanzu haka ake haskawa a YouTube.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button