ASUU Za Ta Janye Yajin Aiki Ba Da Jimawa Ba – Ngige

Ministan Kwadago, Dokta Chris Ngige, ya ce nan ba da jimawa ba yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU ta tsunduma a bayan nan zai zama tarihi.

Dokta Ngige ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin ganawa da manema labarai bayan an kwashe sa’o’i kusan 8 suna tafka mahawara tsakanin shugabannin malaman da wakilan gwamnatin tarayya.

Rahotanni sun ce akwai alamun an fara fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu, inda gwamnatin ta kafa sabon kwamiti tare da shimfida wa’adin makonni shida don ganin an cimma muradun fusatattun malaman jami’o’in.

Ministan ya ce bangarorin biyu sun cimma matsaya a kan batutuwa da dama, kuma shugabannin malaman sun ce, za su je su gabatar da tayin da gwamnati ta musu domin janye yajin aikin.

Ngige ya ce, sun cimma matsaya akan batutuwa da dama, yayin da ma’aikatar ilimi ta kafa wani kwamiti domin nazari akan sauran batutuwan da suka rage.

Ministan ya bayyana cewar gwamnati ta bai wa malaman fiye da naira biliyan 92 daga cikin alawus din da suke bukata na bunkaa jami’o’in kamar yadda yarjejeniyar watan Disambar shekarar 2020 ta gindaya.

A nata bangaren, Kungiyar Malaman Jami’o’in ta ASUU ta ce, za ta koma wurin ’ya’yanta domin bayyana musu tattaunawar da suka yi da gwamnati da zummar janye yajin aikin da suke yi domin daukar matsayi akai.

Shugaban Kungiyar Malaman Farfesa Emmanuel Osodoke ya ce za su je su yi wa ’ya’yan kungiyar bayani akan ganawar da suka yi kafin bayyana matsayin su ga jama’a.

Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar 14 ga wata Fabrairun da a gabata ne Kungiyar ASUU ta sanar da shiga yajin aiki na wata guda domin jan kunne gami da zargi gwamnati da gazawa a cika alkawuran da ta yi wa kungiyar tsawon shekaru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button