Kalaman Sarkin Waka: Mun yi dawafi a kanka, mun hada ka da Allah, Jarumai maza a Saudiyya

Batun rigimar Sarkin Waka da Nafisa Abdullahi, duk da dai wadanda suka fara rigimar sun yi shiru, wasu daga cikin ‘yan masana’antar shirya fim basu bar maganar ba.

Har yanzu a nan da chan ana dan jin maganganu da rubuce-rubuce na nuna rashin jin dadin abinda sarkin wakan ya yi ga ‘yan uwansa ‘yan fim yayin da magoya bayansa na nasu rubutun musamman a Facebook da tiktok.

Yayin da mafi yawan ‘yan kannywood da suka halarci Saudiyya suka ki tofa nasu albarkacin bakinsu suka mayar da hankali kan ibadunsu, Malam Ibrahim Sharukhan, Sani Candy, Suleiman Costume da mai haska dandali kuma jarumi Adebo, sun bayyana cewa sun yi dawafi kuma sun kai karar Naziru wurina Allah kan abinda yake musu.

Kamar yadda Malam Ibrahim Sharukhan yace:

“Da kai nake, Allah yasa kana ganewa. Wallahi, wallahi, wallahi muna garin ma’aiki kuma mun yi dawafi mun hada ka da Allah, munbar ka da Allah.”

Sauran wadanda suka tofa albarkacin bakinsu a kan lamarin a cikin bidiyon da Malam Ibrahim Sharukhan ya saki a shafinsa na Instagram, sun hada da jarum kuma mai haska dandali, Adebo, Sani Candy da Suleiman Costume.

Source: Legit Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button