Kullun burinka ka zagi yan fim: Maryam Booth ta yi martani ga Naziru sarkin waka

Shahararriyar jarumar Kannywood, Maryam Booth ta shiga sahun masu adawa da iyayen da ke tura yaransu wani waje da sunan almajiranci.

Related Articles

Sai dai Maryam ta yi shagube ne ga Naziru Sarkin Waka wanda ya fito ya caccaki masu adawa da tura yara almajiranci, harma ta kai ya kwancewa abokan sana’arsa zani kan haka.

Mawakin dai ya ce idan har ana neman wadanda iyayensu suka haife su amma suka kasa kula da su toh a tafi masana’antar fim.

Da alama wannan furucin bai yiwa wasu daga cikin jaruman musamman mata dadi ba.

A wata wallafa da tayi a shafinta na Instagram, Booth ta saka bidiyon wani malami yana wa’azi a kan mutanen da ke haihuwar yara da yawa alhalin basu da hanyar shigowar kudi a duk wata don kula da su.

A kasan bidiyon, ta rubuta cewa tana jira abawa malamin amsa shima kamar yadda aka yiwa abokiyar sana’arta, Nafisa Abdullahi, wacce dama tun farko ita ce ta fara kalubalantar iyayen da ke tura yara almajiranci.

ta kuma bayyana cewa kafin su su fada malamai ne suka fara fadi amma shi Naziru kullun burinsa shine ya zagi yan fim.

Ta ce:

“Don Allah Ina jiran abawa malam answer shima. Ko dai dama mata kawai za ka iya mayarwa martani? Dan Allah ku tayani fassara masa don na tabbata yana bukatar haka.✌️”

Ta sake rubuta:

“Kafin mu fada malamai sun fada me yahana kabasu answer? Kullim burinka ka zagi yan film koma yaya ne ban zo da rigima ba ramadan kareem”

Jama’a sun yi martani

usman_nasirh ya ce:

“Xafa mu kara sakin video tamm”

ana_herleemerh ta yi martani

“Abin ai da rainin wayo, Sanusi Lamido ma yayi Alla-wadai da almajiranci amma har yau babu wanda ya kalubalance shi”

hannafi_dahiru_kagadama ya ce:

“Wanna magana haka yake Kanwata Ramadan Kareem”

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button