’Yan Sanda Sun Kama Dan Da Ya Kashe Mahaifinsa Saboda Ya Ci Gado

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Neja, ta cafke wani matashi mai shekara 25 da ake zargi da hada baki da abokinsa wajen kisan mahaifinsa saboda ya ci gadonsa.

Matashin, mai suna Abubakar Buba, a cewar rundunar a cikin wata sanarwa, ya kashe mahaifin nasa mai suna Alhaji Mohammed Buba, kuma an kama shi ne a Chanchaga da ke Minna, babban birnin Jihar.

A cewar sanarwar, wacce kakakin rundunar ya fitar, “A ranar 29 ga watan Disamban 2021, da misalin karfe 10:30 na safe, jami’anmu da ke ofishinmu na Chanchaga, bayan samun bayanai, sun cafke wani mai suna Abubakar Mohammed Buba, mai shekara 25 da ke Gidan Madara a yankin Chanchaga na birnin Minna.

“An kama matashin ne bisa zargin aikata kisan kai ga mahaifinsa, Alhaji Mohammed Buba, mai shekara 52.

“Ana zargin an kama tare da kashe mutumin a gidansa da ke Korokpan a Karamar Hukumar Paikoro ranar 13 ga watan Oktoban 2021.”

Ya ce sakamakon tuhumar da aka yi masa, wanda ake zargin ya amsa cewa ya hada baki da abokinsa, wanda yanzu haka ya cika wandonsa da iska, wajen kashe mahaifin nasa.

Kakakin ya kuma ce wanda ake zargin ya jagoranci jami’ansu zuwa madatsar ruwan Tagwai, inda ya jefar da gawar mahaifin nasa bayan ya kashe shi sannan ya jefar da shi a cikin buhu.

“Ya kuma amsa cewa ya dauki hayar abokin nasa mai suna Aliyu Mohammed a kan Naira 110,000, inda ya ba shi kafin alkalamin N50,000, daga bisani kuma ya cika masa N60,000 bayan ya sayar da wasu kadarorin mamacin.

“Ya yi ikirarin cewa ya aikata ta’asar ne don ya samu damar gadon mahaifin nasa cikin gaggawa.

“Muna nan muna kokarin kama Aliyun wanda yanzu ya riga ya gudu, kuma yanzu lamarin na hannun Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar da ke Minna, kuma za a gurfanar da su gaban kuliya da zarar an kammala bincike,” inji Kakakin.

Source: Aminiya Dailytrust


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button