Abdul D One Zai Saki Sabbin Album Dinsa Na 2021

Fitaccen mawakin soyayya na Kannywood wanda akafi sani da Abdul D One yana mai sanar da masoyansa zai saki sabbin album dinsa a kasuwa na shekarar 2021 masu taken suna “NABEELA” Da kuma “Shalele”.

Album mai suna NABEELA zai zo ne a daukar Audio Album shikuma album din Shalele zai zo ne a daukar Video Album.

Abdul D One – NABEELA Audio Album Full Ep 2021

Abdul D One – Shalele Video Album Full Ep 2021

Ya sanar da hakane a shafinsa na Instagram mai suna realabdul done,  wanda haka yasa mutane da dama suna jiran lokacin da wannan mawaki zai saki album amma a cewar wannan mawaki yace zai saki wannan album ranar Laraba 15 September 2021.

Yace kuma Insha Allahu masoyansa zasu sami wannan album a gurin yan tebir da kuma babbar kasuwar nan da ake kira Kofar wambai ta Jihar Kano.

Kuma yace mutane dake sauran garuruwa zasu iya dubu inda yafi kusa dasu domin suma su sami wadannan sabbin album masu taken suna NABEELA da kuma Shalele.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button