Nigeria:Ibrahim Badamasi Babangida(IBB) Ya Bayyana Mataimakin Shugaban Nigeria a Matsayin Wanda Ya Kamata Ya Gaji Buhari.

Nigeria:Ibrahim Badamasi Babangida(IBB) Ya Bayyana Mataimakin Shugaban Nigeria a Matsayin Wanda Ya Kamata Ya Gaji Buhari.
Tsohon shugaban Nigeria a mulkin Soja wato Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana Wanda ya kamata ya gaji nigeria.
Tsohon shugaban ya bayyana Mataimakin shugaban kasar wato Vice-President Yemi Osinbajo na yanzu a Wanda ya kamata ya gaji mulkin kasar.
Gidan jaridar Premiumtimes ta bayyana cewa tsohon shugaban Nigeria ya bayyana hakan Bayan da kungiyar Osinbajo Grassroots Organisation ta ziyarce shi a gidan sa dake Minna.
Sannan kuma ya bayyana Mataimakin shugaban a jajirtacce Sannan kuma ya cancanta domin yadda yake da bada mahimmanci ga ci gaban Yan kasa Sannan ya cancanta ya zama Dan takarar shugaban a 2023.
Ya Kara da cewa nasan Mataimakin shugaban kasar, mutumin kirki ne, da kuma San Habaka tattalin arzikin kasa don haka shine ya kamata ya fito a matsayin dan takarar nigeria.
Sannan tsohon shugaban ya fadama ma organization cewa ya tsaya magana dasu ne sabo da yasan Mataimakin shugaban kasar a matsayin Shugaba na gari.