Wata Kotu a jihar Gombe ta ci saurayi tarar Miliyan 2.6 saboda yaki Auren Budurwar sa

Daga: Yushau Garba Shanga

Wata kotun majistiret da ke da zama a Kumo fadar ƙaramar hukumar Akko a jihar Gombe ta yanke wa wani matashi hukuncin taran N2.6mn sakamakon yaudarar wata budurwar sa har na tsawon shekaru bakwai.

Budurwar ta yi ƙaran tsohon saurayin nata gaban kotun ne domin neman kotu ta bi mata haƙƙin ta tare da shaida mata cewa sun shafe shekara bakwai suna soyayya kwatsam sai ta samu labarin zai auri wata da ba ita ba.

Tuni alƙalin wannan kotu ya umarci wannan saurayi da ya biya ta zunzurutun kuɗi har N2.6m ko kuma ya aureta ko ya tafi gidan gyaran hali na tsawon shekaru 8.

A bangaren saurayin, ya zabi ya fasa auran wacce akasa musu rana domin aurar tsohuwar budurwar sa da ta yi ƙarar sa.

Lallai idan har kotuna za su rika yin irin wannan hukunci samari za su rage yaudara.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button